Wani magidanci ya tsere bayan ya banka wa masoyiyar sa da ‘ya’yanta biyu wuta saboda wani sabani

Wani magidanci ya tsere bayan ya banka wa masoyiyar sa da ‘ya’yanta biyu wuta saboda wani sabani

Wani mutumin kasar Indiya, Jalil Khan, ya banka wa masoyiyarsa, Sangita Suresh Devre, tare da ‘ya’yanta biyu wuta, kamar yadda ‘yan sanda suka sanar a a yau, Litinin.

Khan ya cinna wa Devre wuta ne tare da wata diyar ta dake da aure da kuma jariri saboda wani karamin sabani day a shiga tsakaninsu.

A yayin da jaririn mai watanni 9 a duniya ya mutu, Devre da babbar yarinyar ta sun samu munanan raunuka sakamakon konewar da suka yi. Yanzu haka an kwantar da su a wani asibiti mai zaman kansa, Nashik Civil Hospital, inda aka bayyana yanayin da suke ciki a matsayin mai munin gaske, kamar yadda jami’in ‘yan sanda Madhukar Kad, ya sanar.

Wani magidanci ya tsere bayan ya banka wa masoyiyar sa da ‘ya’yanta biyu wuta saboda wani sabani

Wani magidanci ya tsere bayan ya banka wa masoyiyar sa da ‘ya’yanta biyu wuta saboda wani sabani

Yanzu haka Khan ya cika wandonsa da iska tun bayan aika-aikar da ya yi.

Khan da Derve sun shafe fiye da shekara daya suna cin holewa a matsayin masoya duk da cewar yana da aure. Sun samu sabani ne da ya kai su da yin muhawara mai zafi ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: Wani matashi ya kashe mahaifinsa a masallaci yana cikin sallah

‘Yan sanda sun bayyana cewar Khan ya dawo gidan Devre da talatainin dare tare da kwara wa Devre da diyar tad a kuma jikanta kalanzir sannan ya cinna masu wuta.

Har yanzu ana kokarin gano inda Khan ya shiga domin a kama shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel