APC ta shirya ganin fushin yan Najeriya a 2019 – Sanata Hunkuyi

APC ta shirya ganin fushin yan Najeriya a 2019 – Sanata Hunkuyi

Sanata Suleiman Othman Hunkuyi mai wakiltan Kaduna ta arewa yace jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kuntatawa yan Najeriya don haka ta shirya ganin fushin mutane a 2019.

Ya bayyana hakan a bikin tarban masu sauya sheka da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) babin jihar Kaduna ta shiya a harabar Trade Fair dake Kaduna a ranar Litinin.

APC ta shirya ganin fushin yan Najeriya a 2019 – Sanata Hunkuyi

APC ta shirya ganin fushin yan Najeriya a 2019 – Sanata Hunkuyi
Source: Instagram

Hunkuyi wanda ke maida martani a madadin saura masu sauya sheka yace "Allah ke bayar da mulki amma gwamnatin APC a Kaduna da Najeriya ta kuntatawa jama’a don haka zasu nuna fushin su a lokacin da ya kamata.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugabannin majalisar dokokin kasa za su gana a gobe

“Ba ma zagi amma muna fadin gaskiya. Ina fdama El-Rufai yayi amfani da lokacin da ya rage masa akan mulki don hada kayyayakinsa sannan ya shirya barin gidan gwamnati. Ba ma zagi,amma suna jin ciwo ta hanyar fadin gaskiya da muke yi."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel