Canjin sheka: Mataimakin gwamnan jihar kudu ya musanta komawa APC

Canjin sheka: Mataimakin gwamnan jihar kudu ya musanta komawa APC

Mataimakin gwamnan jihar Akwa Ibom, Moses Ekpo, ya musanta rahotannin dake yawo a gari na cewar ya ajiye mukaminsa tare da komawa jam'iyyar APC.

Mista Ekpo ya bayyana hakan ne ta bakin Ekikere Umoh, sakatarensa na yada labarai yayin ganawa da manema labarai a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar Ekpo ya shaida mata cewar labarin yin murabus da canja sheka ba gaskiya bane a wata tattaunawar su ta wayar tarho.

Zargin komayar Mista Ekpo zuwa APC mai mulki ya biyo bayan komawar tsohon gwamnan jihar kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai, Godswill Akpabio, zuwa jam'iyyar.

Canjin sheka: Mataimakin gwamnan jihar kudu ya musanta komawa APC

Mataimakin gwamnan jihar kudu ya musanta komawa APC

Babban mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin da suka shafi majalisar dattijai, Ita Enang, ne ya tabbatar da komawar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, zuwa jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Mataimakin gwamnan jihar Kano ya ajiye mukaminsa, karanta wasikar

Enang ya sanar da hakan ne ranar Asabar, a shafinsa na Tuwita tare da bayyana cewar za a yi bikin karbarsa ranar 8 ga watan Agusta a jiharsa ta Akwa Ibom.

Ina mai tabbatar da tabbatarwa da jam’iyyar APC cewar, kamar yadda muka bayyana a baya, za a karbi Godswill Akpabio zuwa APC a ranar 8 ga watan Agusta a jihar Akwa Ibom”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel