Da duminsa: Bayan ganawa da Buhari a Ingila, Akpabio ya gana da Tinubu da yamman nan

Da duminsa: Bayan ganawa da Buhari a Ingila, Akpabio ya gana da Tinubu da yamman nan

Bayan takakkiya har birnin Landan doin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari jiya Lahadi, shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, ya garzaya wajen babban jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu.

Sanata Godswill Akpabio ya gana da Bola Tinubu da yammacin yau Litinin, 6 ga watan Agusta a birnin tarayya Abuja.

Da duminsa: Bayan ganawa da Buhari a Ingila, Akpabio ya gana da Tinubu da yamman nan

Da duminsa: Bayan ganawa da Buhari a Ingila, Akpabio ya gana da Tinubu da yamman nan

An yi wata ganawa tsakanin shugaba Muhammadu Buhari dsa shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, a kasar Ingila.

KU KARANTA: Fitar Saraki, Tambuwal da Ortum ba zai hana Buhari cin zabe ba - APC

Idan baku manta ba, a ranan Asabar, ne mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisar dattijai, Ita Enang, ya tabbatar da cewar Akpabio ya canja sheka daga PDP zuwa APC har ya sanar da cewar za a yi bikin karbar sa ranar 8 ga watan Agusta da muke ciki.

Tsohon gwamna Akpabio na daga kusoshin jam'iyyar PDP a yankin kudu maso kudu mai arzikin man fetur.

Akwai rahotannin cewar wasu gwamnoni PDP daga kudancin Najeriya zasu koma APC kafin zaben 2019.

Da duminsa: Bayan ganawa da Buhari a Ingila, Akpabio ya gana da Tinubu da yamman nan

Da duminsa: Bayan ganawa da Buhari a Ingila, Akpabio ya gana da Tinubu da yamman nan

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel