An fara: An shiga wata ganawar sirri tsakanin mukaddashin shugaban kasa da shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai

An fara: An shiga wata ganawar sirri tsakanin mukaddashin shugaban kasa da shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai

Rahotanni da jaridar Legit.ng ta samu sun tabbatar da cewar yanzu haka ana can an shiga wata ganawar sirri tsakanin mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Ya zuwa yanzu ba a san dalilin wannnan ganawa ba, kazalika fadar ta shugaban kasa ba ta fitar da wata sanarwa dangane da ganawar ba.

Tun a satin da ya gabata ne batun tafiyar shugaba Buhari hutu kasar Ingila ya saka jam’iyyar adawa ta PDP cikin tararrabi tare da zargin cewar Buhari zai fice daga Najeriya ne bayan ya kamala kitsa yadda za a cire shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, saboda ya fita daga jam’iyyar APC.

An fara: An shiga wata ganawar sirri tsakanin mukaddashin shugaban kasa da shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai, Ahmed Lawan

A wani jawabin PDP ta fitar ta bakin sakataren ta na yada labarai, Kola Ologbondiyan, jam’iyyar ta ce tana sane sarai da makircin da shugaba Buhari ya gama kullawa tsakaninsa da gwamnoni da kuma Sanatocin APC domin tsige Bukola Saraki.

DUBA WANNAN: Mataimakin gwamnan Kano ya ajiye mukaminsa, karanta wasikar da ya rubuta

Wasu masu nazarin siyasa na ganin cewar Farfesa Osinbajo tare da wasu jiga-jigan 'ya'yan APC zasu tsige Bukola Saraki kafin dawowar shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel