Ba zan tsaya ganin laifin shugabannin baya ba idan aka zabe ni matsayin shugaban kasa - Dankwambo

Ba zan tsaya ganin laifin shugabannin baya ba idan aka zabe ni matsayin shugaban kasa - Dankwambo

Gwamnan jihar Gombe kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 mai zuwa, Ibrahim Dankwambo yayi alkawarin cewa ba zai tsaya wasar ganin laifi ba idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Koda dai Dankwambo bai ambaci sunan kowa ba, amma ana yawan sukar gwamnati mai ci ta shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yawan ganin laifin tsoffin shugabannin Najeriya kan matsalolin Najeriya don haka babu mamaki da ita yake.

“A matsayin shugaban ku, ba zan ga laifin kowa akan matsalolin Najeriya ba, zan magance su. An zabi shugabanni ne domin su magance matsaloli,” cewar Dankwambo a shafin twitter.

Ba zan ga laifin shugabannin baya ba idan aka zabe ni matsayin shuaban kasa - Dankwambo

Ba zan ga laifin shugabannin baya ba idan aka zabe ni matsayin shuaban kasa - Dankwambo

A kwanakin baya ne Dankwabo ya nuna ra’ayinsa na son takarar shugaban kasa karashin jam’iyyar PDP.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka: Osinbajo da Oshiomhole na shirin hargits majalisar dokoki – Majalisar wakilai

Sai dai kimanin su goma sha biyu ke farautar kujerar a karkashin PDP inda ake sanya ran za’a yi zaben fid da gwani a watan Nuwamba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel