Yanzu Yanzu: Mataimakin shugaban APC na Osun ya jagoranci mutane 6,208 zuwa ADP

Yanzu Yanzu: Mataimakin shugaban APC na Osun ya jagoranci mutane 6,208 zuwa ADP

Mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress a jihar Osun, Azeez Adesiji, ya jagoranci mambobin kwamitin jam’iyyar na jihar su takwas da mambobin jam’iyyar 6,200 na kananan hukumomi da mazabu zuwa jam’iyyar Action Democratic Party.

Shugabannin APC da mabiyansu sun samu tarba daga shugaban jam’iyyar APD, Toye Akinola a sakatariya jam’iyyar dake Osogbo cikin farin ciki.

Adesiji yayi zargin cewa dalilin su na sauya sheka ya kasace saboda son kai da halin rashi kula na masu yanke hukunci a APC da kuma yadda gwamnatin jhar ke yi da jama’a ajihar.

Shugaban jam’iyyar ADP a jihar, Toye Akinola yace ya ji dadin sauya shekar yan siyasa daga jam’iya mai mulki zuwa jam’iyyar adawar.

KU KARANTA KUMA: Hankulan shugabannin siyasa bai kwanta da gwamnatin Buhari ba - Okorocha

Yace wasu yan jam’iyyar APC sun sanar da shi cewa suna nan dawowa jam’iyyar kwanan nan.

Ya bukaci mutanen jihar da su marawa dan takarar gwamna a jam’iyyar Moshood Adeoti vaya domin cewa shine zai ceto su daga wahalhalun da suke ciki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

\

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel