Hankulan shugabannin siyasa bai kwanta da gwamnatin Buhari ba - Okorocha

Hankulan shugabannin siyasa bai kwanta da gwamnatin Buhari ba - Okorocha

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana cewa hankulan shugabannin siyasa a kasar bai kwanta da gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ba don haka suka hade masa kai.

Gwamnan wadda ya kara da cewa shugaban kasar bai aikata aibu a garesu ba, ya bayyana cewa shugabanni na tsoron a hukunta su akan rashawar da suke yi hakan ne yasa suka hadewa shugaban kasar kai.

Hankulan shugabannin siyasa bai kwanta da gwamnatin Buhari ba - Okorocha

Hankulan shugabannin siyasa bai kwanta da gwamnatin Buhari ba - Okorocha

Gwamnan yace shugaban kasar ya yarda da al’umma sannan kuma ya yarda cewa dole a yi taka tsantsan da arzikin kasar don jama’a su amfana daga gare shi, inda ya kara da cewa wadannan dalilai ne yasa shugabannin suke ganin bakin Buari sannan suna aikata hakan ne domin son zuciyarsu.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka: Osinbajo da Oshiomhole na shirin hargitsa majalisar dokoki – Majalisar wakilai

Gwamnan ya kara da cewa ya zama dole yan Najeriya su marawa shugaba Buhari baya domin yayi korari sosai wajen tsayawa kan gaskiya kuma bai amince da yin almubazaranci da dukiyar jama’a ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel