Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindigar jihar Benuwe

Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindigar jihar Benuwe

Dakarun Sojin Najeriya na rundunar mayakan Sojan kasa sun yi arangama da yan bindiga makiyaya dake addabar jama’an jihar, a daidai garin Gbajimba-Akor, cikin karamar hukumar Guma, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Sojojin sun samu nasara akan yan bindigan bayan kwashe awanni da dama ana musayar wuta, daga nan yan bindigan suka ranta ana kare, wanda hakana ya baiwa Sojojin daman lalatawa tare da babbaka sansanoninsu.

KU KARANTA: Zakaran gwajin dafi: Dalibi daga Arewacin Najeriya ya yi zarra a jarabawar JAMB Kaakakin rundunar Sojan kasa, Texas Chukwu ne ya sanar da haka a ranar Litinin, 6 ga watan Agusta, inda yace lamarin lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 4 ga watan Agusta, kamar yadda mjiyar Legit.ng ta ruwaito.

Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindigar jihar Benuwe

Sansanin yan bindigar jihar Benuwe

“Sojoji sun ci karo da yan bindiga makiyaya tare da garke garke na shanu, inda aka yi ta musayarwa wuta, amma daga bisani ganin cewa Sojoji sun fi karfinsu, sai yan bindigan suka tsere wasu da raunuka a tare dasu, yayin da dama suka fadi matattu, amma a yanzu haka muna farautar wadanda suka tsere.” Inji shi.

Birgediya Chukwu yace Sojoji sun kwato bindigu da suka hada da AK 47 guda uku, alburusai da babura guda biyar, sa’annnan ya yi kira ga jama’a dasu taimaka ma hukumomin tsaro da bayanan sirri game da take taken duk mutumin da basu gane ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel