Tun kafin ai nisa EFCC ta fara bincikar Fayose da matarsa

Tun kafin ai nisa EFCC ta fara bincikar Fayose da matarsa

- Zancen bincikar Fayose da EFCC tayi alwashin yi na dafa da kankama

- A kwanan baya ne dai bayan faduwa zaben dan takarar da ya tsayar hukumar ta wallafa a shafinta na Twita cewa da sannu zai shigo hannunta

Yanzu haka dai wasu alamomi tun a jiya sun nuna cewa hukumar EFCC ta fara bincikar gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose tare da mai dakinsa Feyisetan da kuma wasu jiga-jigai na gwamnatinsa.

Tun kafin ai nisa EFCC ta fara bincikar Fayose da matarsa

Tun kafin ai nisa EFCC ta fara bincikar Fayose da matarsa

Manema labarai sun yi kokari wajen samun sakataren gwamnan Idowu Adelusi ta waya domin jin ta bakinsa, amma shiru kake ji kamar an shuka dusa domin yaki daga wayar balle a ji ta bakinsa.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa daga cikin mutanen da hukumar take bincike akwai mai magana da yawun gwamnan Lere Olayinka, kwamishinan kudi Toyin Ojo tare da akanta janar na jihar Oluyemisi Owolabi.

KU KARANTA: Ficewar Saraki daga jam’iyyar APC tamkar mutuwar jam’iyyar ne ― Balarabe Musa

Rahotanni sun gabata cewa za a tuhumi gwamnan shi da matarsa da kuma mukarrabansa akan laifin karkatar da wasu kudi ba bisa ka'ida ba tare da laifin tafiyar da harkokin ofishin gwamna ta hanyar da bai kamata ba.

Kamar jaridar Cable ta ganewa idonta daya daga cikin wasu wasiku da gwamnan ya aikewa manajan bankin Access tun a 20 ga watan Yuli 2018, ya nuna cewa hukumar tana kan bincikar gwamnan domin gano wasu badakala da ake zarginsa da aikatawa.

Tun kafin ai nisa EFCC ta fara bincikar Fayose da matarsa

Tun kafin ai nisa EFCC ta fara bincikar Fayose da matarsa

Hukumar ta EFCC ta bayyana cewa akwai asusun banki har guda hudu da take bincike akansu wanda ana zargin cewa na gwamnan ne.

Har wa yau akwai asusun banki har guda biyar wanda ake zargin na mai dakin gwamnan ne duka a bankin na Access.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta EFCC ta aikewa da bankin takardar gayyatar wasu jami'an bankin zuwa ofishinta domin amsa wasu tambayoyi tun ranar 24 ga watan Yuli 2018.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel