Kwamishina da wasu mutane 4 na hararar kujerar mataimakin gwamnan Kano

Kwamishina da wasu mutane 4 na hararar kujerar mataimakin gwamnan Kano

Bayan ajiye aikin mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar a ranar Lahadi, yan takara da dama sun nuna ra’ayinsu na son maye gurbinsa.

Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnatin jihar, ta bayyana cewa zuwa yanzu kimanin yan takara biyar ne ke fafutukar maye gurbin mataimakin gwamnan.

Shahararru a cikinsu, bisa ga bincikenmu sun hada da kwamishinan bayanai mai ci, Malam Muhammad Garba wadda ya taba shugabantar kungiyar NUJ, kuma tsohon abokin Gwamna Abdullahi Ganduje wadda ya fito daga yankin Kano ta sakiya, mazaba daya da tsohon mataimakin gwamnan.

Kwamishina da wasu mutane 4 na hararar kujerar mataimakin gwamnan Kano

Kwamishina da wasu mutane 4 na hararar kujerar mataimakin gwamnan Kano

Sauran sun hada da kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Kabiru Al-Hassan Rurum, tsohon kakakin majalisar jihar, Abdullahi Yusuf Ata da Abdullahi Abbas, shugaban APC na jihar, da kuma Sheikh Ibrahim Khaliel, wadda kungiyar lamai na Kano ke so.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka: Osinbajo da Oshiomhole na shirin hargits majalisar dokoki – Majalisar wakilai

Sai dai hasashe sun nuna cewa ga dukkan alamu matsayin na iya zuwa ga Malam Garba wadda ya kasance babban dan adawan Kwankwaso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel