Sauya sheka: Osinbajo da Oshiomhole na shirin hargitsa majalisar dokoki – Majalisar wakilai

Sauya sheka: Osinbajo da Oshiomhole na shirin hargitsa majalisar dokoki – Majalisar wakilai

Mambobin majalisar wakilai karkashin lemar kungiyar damokradiya na majalisar wato Parliamentary Democrats Group (PDG) sun zargi mataimakin shugaban kasa Osinbajo da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, da daukar nauyin wasu sanatocin APC wajen haifar da hargitsi a majalisar dokokin kasar.

Da yake hira da manema labarai a Abuja, kakakin kungiyar ta PDG, Timothy Golu (PDP, Plateau), yayi zargin cewa “Wadannan sanatocin na APC wanda Osinbajo da Oshiomhole suka baiwa makudan kudade sun yanke shawarar taka yan majalisan da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a kwanan nan.”

Yan majalisan sunce sun mamakin cewa Osinbajo da Oshiomhole na iya bayar da irin wannan makudan kudade daga asusun gwamnati don siye sanatoci da mambobin majalisar wakilai saboda adawa da shugabannin majalsun guda biyu.

Sauya sheka: Osinbajo da Oshiomhole na shirin hargits majalisar dokoki – Majalisar wakilai

Sauya sheka: Osinbajo da Oshiomhole na shirin hargits majalisar dokoki – Majalisar wakilai

Kungiyar ta nuna kulawa kan yunkurin da gwamnatin APC ke yi wajen son hallaka damokradiyar Najeriya, inda suka yi gargadi cwa bazasu yarda da wannan yunkuri ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan Akwa Ibom yayi murabus, ya koma APC

Sun kuma yi kira ga yan Najeriya da su rike martaba, ka’ida da kuma yancin majalisar dokoki don tabbaar da cewa dukkanin mambobin sun yi mu’amala kai tsaye da jam’iyyun siyasa domin su samu damar isar da dimokradiya ga mazabunsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel