APC ta ce lallai sai ta tsige Saraki, ta bayyana matakin da za ta dauka

APC ta ce lallai sai ta tsige Saraki, ta bayyana matakin da za ta dauka

Jam’iyyar All Progressives Congress APC ta jaddada kudirinta na son tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki daga kan kujerarsa, amma tace maimakon kashe miliyoyin naira na jama’a akan lamarin, zata yi amfani da karfinta na masu rinjaye wajen tsige Saraki daga gabanta.

Jam’iyyar na maida martani ga tuntubar da kafofin watsa labarai sukayi game da zargin da gamayyar kungiyar, wato sabuwar APC tayi na cewa jam’iyyar na amfani da kudin jama’a waje akai.

“Duk ihun mutumin da ya rigada ya nitse a kogi ne. Kassim Afebua da makuarrabansa na kokarin amfani da son zuciya ne da kuma yunkurin zubar da martabar gwamnatin APC ,” Yekini Naena, mukaddashin sakataren labaran APC ya fadi akan zargin da R-APC ke yi.

APC ta ce lallai sai ta tsige Saraki, ta bayyana matakan da za ta dauka

APC ta ce lallai sai ta tsige Saraki, ta bayyana matakan da za ta dauka

Nabena yace dalilin da yasa mafi akasarinsu ke sauya sheka saboda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bata raba kudi wadda shine kafin gwamnatin PDP.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da ya sa mataimakin gwamnan Kano Hafiz Abubakar yayi murabus - Kwamishina

A halin da ake ciki, Pa Moses Ekpo, mataimakin gwamnan jihar Akwa Ibom yayi murabus, kamar yadda shafukan @APCNewspaper da Ibom.com.ng suka wallafa a twitter.

Gwamnatin PDP mai mulki a Akwa Ibom bata tabbatar da hakan ba tukuna, amma APC da Ekpo, mataimakin gwamna mafi dadewa a Najeriya, na kokarin bin sahin Sanata Godswill Akpabio zuwa jam’iyyar All Progressives Congress.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel