Tsaro: Boko Haram ta sake kashe mutane a Maidugiri da safen nan

Tsaro: Boko Haram ta sake kashe mutane a Maidugiri da safen nan

- Har yanzu ba'a gama da Boko Haram ba

- Gwamnati na iya yinta, amma malamai ma na can suna zafafa wa jama'a ra'ayi

- Addinin Islama ne ya kawo jihadi a kasar hausa

Tsaro: Boko Haram ta sake kashe mutane a Maidugiri da safen nan

Tsaro: Boko Haram ta sake kashe mutane a Maidugiri da safen nan

Masu harin kunar bakin wake har 5 ne suka kai hari a daren jiya a birnin Maiduguri ta jihar Borno, wadda ta shafe shekaru akalla 9 tana fama da masu jihadin Islama, wai sai sun tabbatar da shari'ar Islama wadda ko Larabawa basu yi a kasashen su.

A kokarin gwamnatin Najeriya na dakile shirin, an kai soji kbirnin an kuma sake sauya manyansu a kwanakin nan, bayan da aka kashe sojoj akalla 17 a watan jiya a harin sunkuru.

A harin bam din na jiya dai, an kashe mutun biyu, an kuma jikkata uku, wanda hakan ke nuna harin bayyi wata nasara ba, in aka kwatanta da yadda suke zub da jini a baya.

DUBA WANNAN: Rigima tsakanin Canada da Amurka

Harin yazo ne a uguwar Kalari, wadda ke bayan jami'ar Maiduguri ta tarayya, kuma ance ko'ina anji karar fashewar bama-baman a birnin.

A shekarun 2000s dai, jama'ar Arewa na nuna soyayyarsu a fili ga 'yan ta'addar duniya irinsu Usama Bin Laden da Taliban, amma da abin ya zo gida sai suka zame ssuka koma bayan gwamnati da 'yan ta'addan ke kira dagutai.

Ita dai shariar Islama ta ta'allaqa ne da mulkin komai da komai a siyasance, kamar yadda ayoyi a Kur'ani suka kafirta wanda baiyi aiki da ita ba, wanda kuma hakan ya sanya Boko Haram ke kashe musulmin Najeriya, wai ai sun bi dimokuradiyyar Turawa, maimakon tsarin su Danfodio da El-Kanemi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel