Fasinja son koka kan cuwa-cuwa a harkar tikitin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Fasinja son koka kan cuwa-cuwa a harkar tikitin jirgin kasan Abuja-Kaduna

- Duk wani yunkurin Jin ta bakin jami'an bai yuwu ba, amma daya daga cikin ma'aikatan yace mafita itace a kara yawan jiragen kasan dake aiki a ranar lahadi

- Ya bukaci da a boye sunan, yace tsoron tafiya a tituna saboda tsaro yasa mutane ke kara tururuwar tafiya a jiragen kasa

- A lokacin da muka dau wannan rahoton (karfe hudu da minti goma na yamma) sojoji aka turo tashar domin kwantar da tarzomar kafin fasinjojin su shiga jirgin kasan

Fasinja son koka kan cuwa-cuwa a harkar tikitin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Fasinja son koka kan cuwa-cuwa a harkar tikitin jirgin kasan Abuja-Kaduna

A ranar lahadi ne Daruruwan fasinjojin jirgin kasa sukayi zanga zanga sakamakon zargin rashin gaskiya da akeyi gurin siyar da tikitin jirgin kasan Kaduna-Abuja.

Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa duk da jirgin karfe hudu na yamman ya iso akan lokaci, fasinjojin sun hana shiga jirgin kasan a tashar rigasa a jiya lahadi.

Fasinjojin sunce an siyar da tikitin na mintina goma kacal, sai jami'an suka ce tikitin ya kare.

Wani fasinja mai suna, Usman Lamin ya zargi jami'an tashar da siyar da sama da tikiti 600 ta bayan fage ga masu talla inda su kuma suke ninka kudin.

Fasinjojin sunce dole sai dai manajan tashar ya bar kowa ya shiga jirgin, akan hanya sai a karbi kudin ko kuma babu wanda zai shiga.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa Farfesa Hafiz Abubakar ya bar gwamnatin Kano

Duk wani yunkurin Jin ta bakin jami'an bai yuwu ba, amma daya daga cikin ma'aikatan yace mafita itace a kara yawan jiragen kasan dake aiki a ranar lahadi.

Ya bukaci da a boye sunan, yace tsoron tafiya a tituna saboda tsaro yasa mutane ke kara tururuwar tafiya a jiragen kasa.

A lokacin da muka dau wannan rahoton (karfe hudu da minti goma na yamma) sojoji aka turo tashar domin kwantar da tarzomar kafin fasinjojin su shiga jirgin kasan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel