Yadda wani Mutumi ya kashe masoyiyarsa sakamakon gano kwaroron roba a Jakarta

Yadda wani Mutumi ya kashe masoyiyarsa sakamakon gano kwaroron roba a Jakarta

Wani lamari mai ban takaici ya faru a garin Bini na jihar Edo, inda wani mutumi mai suna Osaremwinda Omobude Idumwonyi ya halaka wata Bazawararsa Gladys Oko mai shekaru 38 bayan ya gano kwaroron roba a cikin Jakarta, wanda hakan yasa yake tunanin tana bin maza kenan.

Omobude mai shekaru 46 ya yi amfani da adda inda ya daddatsa Gladys mai yaya uku, a gaban mahaifiyarta, bayan ya gani robobin, sai dai jaridar Daily Nigerian ta ruwaito matar ta bata kwana a gidansu ba, inda ake zargin ta kwana a gidan wani ne daban.

KU KARANTA: An huro ma Tambuwal wuta sai ya yi murabus daga kujerarsa ta Gwamna

Sai dai Ombude ya bayyana ma jami’an Yansanda bayan ya shiga hannunsu cewa ba da gangan ya kashe Gladys ba, inda ya kara da cewa Gladys ce ta fara daukan wuka ta yi kansa bayan cacar baki ya kaure a tsakaninsu.

“Muna cikin wannan taga taga ne, sai kawai na kwace wukar, kuma na caccaka mata har sau uku a cikinta, amma fa tare da na sani ba, ina kokarin kare kaina ne kawai, duk da haka an garzaya da ita zuwa Asibiti, inda bayan yan kwanaki ta cika.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Yansanda jihar Edo sun kama wani matashi mai shekaru 19 a garin Bini da ya kashe budurwasa mai shekaru 18 akan zarginta da cin amanarsa, haka zalika wasu Mazaje biyu sun kashe yan matansu biyo bayan samun labarin suna neman wasu mazan daban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel