Sallamar Shehu Sani: Jam’iyyar APC ta Kaduna ta yi ma Uwar jam’iyya bore

Sallamar Shehu Sani: Jam’iyyar APC ta Kaduna ta yi ma Uwar jam’iyya bore

Shugabancin jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna sun yi ma uwar jam’iyyar APC ta kasa bore bisa batun sallamar wakilin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani daga jam’iyyarsu, duk kuwa da uwar jam’iyyar ta wanke shi soso da sabulu.

A cikin wata sanarwar da Kaakakin jam’iyyar APC, Yekini Nabena ya fitar, yace: “Uwar jam’iyyar ta kasa ta samu labarin sallamar Shehu Sani daga jam’iyyar da shugabancin APC a mazabar ta Tudun Wada ta yi, don haka ina sanar da cewa uwar jam’iyya ta dage sallamar tasa.

KU KARANTA: Haduwar Kwankwaso da Shekarau: Ta ciki na ciki – Inji jam’iyyar APC

“Don haka ya zama cikakken dan jam’iyya, kuma shugaba a jam’iyyar, Uwar jam’iyya ta aika ma jam’iyyar APC na jihar Kaduna umarnin ya fada ma shugabancin APC a matakin karamar hukuma da mazaba, haka zalika an umarcesu dasu yi taimaka ma jam’iyyar wajen kawo zaman lafiya da hadin kai.” Inji shi.

Sallamar Shehu Sani: Jam’iyyar APC ta Kaduna ta yi ma Uwar jam’iyya bore

Shehu Sani
Source: Depositphotos

Sai dai Kaakakin APC ta jihar Kaduna, Salisu Wusono ya bayyana rashin amincewarsu da wannan umarni na uwar jam’iyya, inda yace babu inda kundin tsarin mulkin jam’iyya ya baiwa uwar jam’iyya ikon canza duk wani hukunci da aka dauka a matakin mazaba.

“Don haka muna tabbatar da sallamar da muka yi ma Shehu Sani sakamakon rashin da’a tare da cin mutuncin tsarin mulkin jam’iyyar, don babu yadda za’ayi ka shiga jam’iyya a mazaba, amma ka dinga cin mutuncinta na tsawon shekaru uku, kawai sai mu ji wai uwar jam’iyya ta kasa ta wanke ka, ta kuma kakaba mana kai, ba zai yiwu ba.” Inji Wusono.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Wusono yana cewa Shehu Sani ya yi ma sashi na 21A (i-xi) karan tsaye, ya kara da cewa tun a watan Disambar 2015 jam’iyyar a mazaba ta 6 na Tudun Wada dake karamar hukumar Kaduna ta kudu ta fara tsare tsaren sallamar Sanatan daga APC na tsawon watann 11.

Amma duk da wannan dakatarwa da APC ta yi ma Sanatan, amma bai daina ci mata mutunci ko zaginta ba, balle kuma ya yi da nasanin laifin fay a aikata, don haka jam’iyyar ta sallameshi na har abada.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel