Gaskiyar dalilin da ya sa mataimakin gwamnan Kano Hafiz Abubakar yayi murabus - Kwamishina

Gaskiyar dalilin da ya sa mataimakin gwamnan Kano Hafiz Abubakar yayi murabus - Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano tace Hafiz Abubakar ya ajiye aiki a matsayin mataimakin gwamna a ranar Lahadi domin gujema tsige shi daga kujerarsa.

A wata sanarwa dauke das a hannun kwamishinan bayanai, Muhammad Garba, a yammacin ranar Lahadi, gwamnatin tace Mista Abubakar ya lura da cewa 30 daga cikin 40 na yan majalisar dokokin jihar Kano sun sanya hannu domin fara shirin tsige shi.

Mista Garba yace an so tsige gwamnan saboda zargin karya da zarge-zarge marasa kan gado da ayiwa gwamnatin jihar.

Gaskiyar dalilin da ya sa mataimakin gwamnan Kano Hafiz Abubakar yayi murabus - Kwamishina

Gaskiyar dalilin da ya sa mataimakin gwamnan Kano Hafiz Abubakar yayi murabus - Kwamishina

Jawabin ya zargi Mista Abubakar da yin sharhi da ka iya haddasa rudani musamman a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da ma jihar gabaki daya.

KU KARANTA KUMA: Sallamar Shehu Sani: Jam’iyyar APC ta Kaduna ta yi ma Uwar jam’iyya bore

Kwamishinan yace ikirarin Abubakar na cewa rayuwarsa da na iyalinsa na cikin barazana duk karya ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel