Mai ba Buhari shawara ya roki ‘Yan Majalisa su hakura da dogon hutu su koma aiki

Mai ba Buhari shawara ya roki ‘Yan Majalisa su hakura da dogon hutu su koma aiki

Fadar Shugaban kasar Najeriya ta roki Shugabannin Majalisa su dawo bakin aiki domin ta cigaba da tafiyar da harkokin Gwamnati da ya shafi daukacin mutanen kasar nan baki daya. Akwai yiwuwar tsige Bukola Saraki da zarar an dawo zama.

Mai ba Buhari shawara ya roki ‘Yan Majalisa su hakura da dogon hutu su koma aiki

Mai ba Buhari shawara kan harkokin Majalisa ya roki Saraki su bude ofis

Babban Mai ba Shugaban kasa Buhari shawara kan harkokin Majalisa watau Sanata Ita Enang yayi wannan kira a sa’ilin da ya gana da ‘Yan Jarida a Legas. Yanzu dai an rufe Majalisun kasar an tafi wani dogon hutu har na watanni 2.

Sanata Ita Enang ya nemi Bukola Saraki da Yakubu Dogara su bude Majalisa domin a amince da karashen aikin da ke cikin kasafin kudin bana wandanda su ka hada kudin da za a warewa Hukumar INEC domin harkar zaben 2019.

KU KARANTA: 2019: Wani Gwamnan Arewa ya fito takarar Shugaban kasa a PDP

Har wa yau akwai mukamai a irin su Hukumomin EFCC, ICPC, CBN, da AMCON da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da su Majalisa domin a tantance su. Har yanzu dai Majalisa ba tace komai game da nadin wannan mukamai ba.

Mai ba Shugaban Kasar shawara ya roki Majalisar Dattawa da ta Wakilan Kasar da su duba wannan lamari mai girma su dawo bakin aiki. Ita Enang yace ya san da cewa ‘Yan Majalisar ba su da niyyar azabtar da daukacin al’ummar Najeriya.

Dama dai a irin wannan lokaci ‘Yan Majalisa kan tafi hutu domin su ga Iyalan su, sai dai wannan karo abin yayi kicibis da shirin lokacin zabe don haka ake nema Majalisa ta dage hutun da tayi niyya. Enang yace ba za dai su tursasa Majalisar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel