Yadda Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole yayi amai ya lashe

Yadda Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole yayi amai ya lashe

Mun fahimci cewa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshimhole yayi aman sa ya lashe bayan da wasu manya a Jamiyyar APC mai mulki su ka sauya-sheka su ka koma Jam’iyyar adawa ta PDP.

Yadda Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole yayi amai ya lashe

Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole yayi tafka da warwara

Kwanaki ne sabon Shugaban na Jam’iyyar APC mai mulki Adams Oshimhole yayi kokarin hana Gwamnan Jihar Benuwai watau Samuel Ortom barin APC. Sai dai hakan ya ci tura inda Gwamnan ya fice ya koma Jam’iyyar adawa.

Jim kadan bayan Mai Girma Gwamna Samuel Ortom ya koma PDP sai kuma aka ji Shugaban APC din yana sukar sa. Adams Oshimhole yace sun ji dadi da Gwamnan ya bar APC domin kuwa ba su bukatar irin su a Jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya tayi wa Inyamurai aiki duk da ba su ba Buhari kuri’a a 2015 ba – APC

Haka kuma dai aka yi kafin wasu ‘Yan Majalisa su fice daga Jam’iyyar APC. Shugaban na APC ya jawo Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso sun gana da Shugaban kasa Buhari domin a hana sa barin Jam’iyyar APC.

Shugaban APC Oshimhole ya yabi tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso wanda yace ba APC ce tayi masa hidima ba sai dai ace su su kayi mata. Sai dai kuma bayan Kwankwaso sun koma PDP, Oshimohole ya karyata kan sa da kan sa.

Dama kun san cewa Shugaban APC na kasar watau Oshiomhole ya fito yana neman Inyamurai su marawa Shugaba Buhari baya a zaben 2019. APC tayi wa Inyamurai gorin cewa Buhari yayi aiki duk da ba bai samu wasu kuri’a a 2015 ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel