Ministan labarai ya maidawa Saraki martani na cewa Shugaba Buhari bai yi da shi ba

Ministan labarai ya maidawa Saraki martani na cewa Shugaba Buhari bai yi da shi ba

Jiya mu ka ji labari daga Jaridar Punch ta kasar nan cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta caccaki Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki na maganganun da yayi kwanaki game da Gwamnatin Tarayyar kasar.

Ministan labarai ya maidawa Saraki martani na cewa Shugaba Buhari bai yi da shi ba

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yace Buhari ya ware su

A baya Bukola Saraki yace Shugaba Buhari yayi watsi da mutanen sa da su ka fito daga Jihar Kwara a Gwamnati. Shugaban Majalisar Kasar yace da zarar an samu wani aiki sai dai ya ji labari an mika sa Jihar Katsina ko kuma Legas.

Lai Mohammed wanda Ministan al’adu da na yada labarai a Najeriya ya maidawa Bukola Saraki martani na cewa Buhari bai yi da shi ba. Ministan yace Gwamnatin Tarayya ta ba mutanen Jihar Kwara fiye da 20 ayyuka masu tsokar gaske.

KU KARANTA: Akpabio: Harkar siyasa lissafi ce ba komai ba – Inji Minista Lai Mohammed

Daga cikin wadanda aka ba wadannan ayyuka, bai fi mutum 2 bane rak su ka fito daga wajen Lai Mohammed wanda shi ne Ministan labarai na kasar ba. Ministan yace mutane 20 din da aka zaba duk sun fito ne daga wajen Shugaban Majalisar Kasar.

Ministan yace don haka babu maganar cewa ana fifita wasu bangaren kasar sai dai kurum jama’a na neman hanyar sata. Lai yace duk wanda yake da gardama ya shiga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya duba yadda ake raba mukamai a Najeriya.

Ministan yace an yi adalci wajen bada mukamai inda ya kuma bayyana cewa Saraki ya hada kai ne da Jam’iyyar PDP wajen ganin an wahalar da Gwamnatin Buhari. Lai yace ko da PDP ke rike da Majalisa iyaka rashin hadin kan da za a samu kenan a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel