APC na neman Inyamurai su marawa Shugaba Buhari baya a zaben 2019

APC na neman Inyamurai su marawa Shugaba Buhari baya a zaben 2019

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya tayi kira ga Inyamurai su marawa Shugaba Buhari baya su fito su zabe sa a 2019 domin ayi wa Yankin kasar aiki kamar yadda aka soma a wannan karo na farko.

APC na neman Inyamurai su marawa Shugaba Buhari baya a zaben 2019

Shugaban APC ya fadawa ‘Yan Kudu zu zabi Buhari a 2019

Shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole a wajen wani babban gangami da Jam’iyyar APC ta shirya a Jihar Ebonyi yayi kira ga inyamurai su bi Buhari. Oshiomhole yace idan har mutanen Kudu su ka zabi APC a 2019, za su cigaba da ganin ayyuka.

A makon da ya shude ne Jam’iyyar APC ta shirya wani babban taron siyasa a Garin Abakaliki inda tayi wa wasu tsofaffin ‘Yan PDP da ake ji da su wanka. Daga cikin wadanda su ka dawo APC a Yankin akwai wani Sanata da tsohon Ministan kasar.

KU KARANTA:

Kwamared Adams Oshiomhole ya tunawa mutanen na Kudu maso Gabashin kasar cewa duk da ba su zabi Shugaba Buhari ba yayi masu aiki. Daga cikin ayyukan da aka yi wa Yankin akwai gadar Neja da aka soma da kuma hanyoyi iri-iri.

A kaf Kasar Kudu maso Gabas dai kuri’un da Buhari ya samu a 2015 ba su kai 200, 000 ba inda PDP kuwa ta tashi da sama da Miliyan 2. Shugaban APC yace duk da wannan bai hana ayi masu aiki ba, ina ma kuma ace sun mara masa baya a 2019.

Kwanaki kun ji cewa wani ‘Dan wasan kwaikwayo Keneth Okonkwo yayi kira ga Jama’a su marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa a Kasar Inyamurai. Kenneth Okonkwo yace daga Buhari ya gama sai Inyamurai zai yi mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel