Mataimakin Gwamnan Kano ya fasa kwan dalilan da yasa yayi murabus

Mataimakin Gwamnan Kano ya fasa kwan dalilan da yasa yayi murabus

- Bayan mika takardar ajiye aikin sa a yau, mataimakin gwamnan ya bayyana dalilansa

- Siyasar jihar Kano dai na cigaba da dumama tun bayan komawar Kwankwaso jam'iyyar PDP

- Dama dai mataimakin gwamnan Farfesa Hafiz tuntuni ya bayyana cewa ko da an karasa mulkin shi ba zai yi tazarce a mataimakin gwamnan ba

A yau ne mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya wallafa a shafinsa na twitter cewa ya yi murabus daga kan kujerarsa ta mataimakin gwamnan jihar.

Mataimakin Gwamnan Kano ya fasa kwan dalilan da yasa yayi murabus

Mataimakin Gwamnan Kano ya fasa kwan dalilan da yasa yayi murabus

Dama cikin satin nan ana ta rade-radin cewa Hafiz zai bar jam'iyyar ta APC domin komawa PDP musamman idan aka duba irin alakar dake tsakaninsa da tsohon gwamna Kwankwanso. Sai dai a kwanakin da suka shude Farfesa Hafiz ya musanta zargin da ake cewa zai bar jam'iyyar.

Tsohon mataimakin gwamnan ya wallafa a shafinsa na twitter kamar haka "Ina so in sanarwa da jama'ar Kano cewa a matsayina na mataimakin gwamna na jihar Kano, a jiya ne na aikewa gwamna da takardar barin mukamina" inji Hafiz.

KU KARANTA: Yadda Tambuwal ya ba ni cin hancin Naira miliyan N13m don na bi shi PDP – Dan majalis

Kamar yadda ya wallafa a cikin takardar da ya aikewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce "Mai girma gwamna naso ace na zauna akan kujerar nan domin karasa mulkin da muka faro tun 2015, amma saboda irin sabanin ra'ayi da muke samu a siyasance da kuma yadda ake gudanar da mulkin Kano, bana tunanin zama na zai haifar da da mai ido. Kuma bana tunanin na yiwa kaina da jama'ar Kano adalci da ma kai kanka a matsayinka na shugaba".

Mataimakin Gwamnan Kano ya fasa kwan dalilan da yasa yayi murabus

Mataimakin Gwamnan Kano ya fasa kwan dalilan da yasa yayi murabus

Ganin yadda siyasar shekara ta 2019 ke matsowa jam'iyya mai ci (APC) musamman a Kano sai samun nakasu take yi.

A kwanakin baya dama masu sharhin siyasa suka yi fashin baki game da cewa Hafiz zai iya ficewa daga jam'iyyar saboda irin takun-saka da yake samu da gwamna Ganduje, sannan kuma ga uban gidansa Kwankwaso ya koma jam'iyyar PDP.

Idan ba a manta ba a watannin da suka gabata Hafiz ya taba bayyana cewa ba shi da muradin sake cigaba da tafiya a karkashin jagorancin gwamnatin jihar Kano, inda ya bayyana cewa zai hakura ya koma bakin aikinsa a Jami'ar Bayero dake Kano.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel