Abin tausayi: masu yiwa kasa hidima 9 sun nitse a ruwa a jihar Taraba

Abin tausayi: masu yiwa kasa hidima 9 sun nitse a ruwa a jihar Taraba

- Karar kwana ta kai wasu masu yiwa kasa hidima tafiya zagaya gari

- Daga nan kuma basu sake dowowa gida ba sakamakon nitsewa a ruwa

Wasu masu yiwa kasa hidima (NYSC) guda tara sun nutse a cikin wani ruwa dake karamar hukumar Gashaka a jihar Taraba.

Abin tausayi: masu yiwa kasa hidima 9 sun nitse a ruwa a jihar Taraba

Abin tausayi: masu yiwa kasa hidima 9 sun nitse a ruwa a jihar Taraba

Bayanai sun bayyana cewa 'yan yiwa kasar hidimar sun fita yawan shakatawa ne, sai dai an yi rashin sa'a ruwa ya ci har tara daga cikinsu wanda kawo yanzu an samu gawar mutum hudu.

KU KARANTA: 'Yan sanda a Kano sun bazama neman wadanda su kayi fyade yarinya ga yarinya 'yar shekara 3

Shugaban masu yiwa kasa hidima na jihar ta Taraba Florence Yaakugh, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa har yanzu ana cigaba da kokarin gano ragowar guda biyar din da suka bace.

Jaridar vanguard ta rawaito cewa gawar wadanda aka samu ya zuwa yanzu ta maza biyu da mata biyu ce, wanda suka fito daga jahohin Enugu, Imo, Delta da kuma jihar Edo.

Jim kadan bayan tuntubar mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar ASP David Misal akan lamarin, ya shaidawa manema labari cewa suna da masaniya game da faruwar lamarin.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel