Daga karshe: Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi murabus, karanta wasikar

Daga karshe: Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi murabus, karanta wasikar

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya mika takardar barin mukaminsa a yau, Lahadi, ga gwamna Ganduje.

A takardar tasa ta murabus, mai dauke da kwanan watan yau, 5 ga watan Agusta, ya bayyana cewar ya so ya zauna a ofis har zuwa karshen wannan zangon amma rashin sasanta wasu matsaloli tsakaninsa da gwamna Ganduje ya saka shi yanke shawarar yin murabus.

" Ina mai matukar nadamar sanar da kai cewar na yanke shawarar ajiye mukamina daga ranar 4 ga watan Agusta, 2018."

DUBA WANNAN: Ina daram a APC ban fita ba - Mataimakin gwamnan Kano

"Mai girma gwamna, na so zama tare da kai har zuwa karshen wannan zangon amma wasu rashin sasanta banbancen mu a kan sha'anin mulki da gwamnati da kuma na kashin kai, ya saka ni jin cewar ban yiwa kaina da kai kan ka da jama'ar jihar Kano adalci ba idan na cigaba da zama tare da kai a matsayina na mataimakin gwamnan jihar Kano.

Karanta wasikar

Daga karshe: Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi murabus, karanta wasikar

Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi murabus, karanta wasikar

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel