Kwanan nan za mu tsige Saraki daga Shugaban Majalisar Dattawa – Ndume

Kwanan nan za mu tsige Saraki daga Shugaban Majalisar Dattawa – Ndume

Tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Muhammad Ali Ndume ya bayyana cewa da zarar an dawo hutun da Majalisa ta tafi za a tsige Bukola Saraki daga kujerar sa.

Kwanan nan za mu tsige Saraki daga Shugaban Majalisar Dattawa – Ndume

Jam'iyyar APC ta fi PDP mai mulki yawan 'Yan Majalisu

Sanatan Kudancin Borno, Ndume yace idan an dawo bakin aiki a cikin Watan Satumba za a tsige Bukola Saraki daga kujerar sa. Sanata Ndume ya bayyana wannan ne wajen wani taron siyasa da aka yi a Mahaifar sa Jihar Borno.

Muhammad Ali Ndume yace a dakata a gani, lokaci kurum su ke jira su sauke Bukola Saraki su nada sabon Shugaban Majalisar Dattawa. Sanatan yace tun farko bai halatta ‘Yan Majalisa da Gwamnoni su sauya shekar su ba.

KU KARANTA: Tsohon Gwamnan PDP da ya koma APC kuma ana shirin daura sa a matsayin Saraki

’Dan Majalisar yace duk wanda ya sauya sheka, dole ya bar mukamin sa don haka dole su Bukola Saraki su bar matsayin su. Sanatan na Kudancin Borno yace wasu na barin APC ne zuwa PDP domin gudun a binciki laifin su.

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa duk taron-dangin da ake yi a PDP ba zai hana Shugaban kasa Muhammadu Buhari zarcewa ba. Sanatocin da ke tare da Saraki dai sun ce ba za su bari a nada wani sabon Shugaban Majalisa ba.

Kwanaki kun ji cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ja kunnen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da shirin tsige Shugaban Majalisar Dattawan. Saraki ya koma PDP kwanan nan don haka 'Yan APC ke nema su tsige sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel