Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da 'yan ta'addan Boko Haram

Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da 'yan ta'addan Boko Haram

Rundunar dakarun sojin Najeriya dake sintirin tabbatar da tsaro da samar da zaman lafiya a jahohin Arewa ta gabas a ranar Alhamis din da ta gabata sun sanar da yin kicibis da wasu 'yan ta'addan Boko Haram a kauyen Malari na jihar Borno.

Sanarwar afkuwar hakan dai ta fito ne dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na hedikwatar rundunar dake Abuja, Texas Chuku inda yace kuma dakarun nasu sun yi dauki ba dadi da 'yan ta'addan inda suka kashe wasu da dama sannan kuma wasun su suka tsere cikin daji.

Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da 'yan ta'addan Boko Haram

Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da 'yan ta'addan Boko Haram

KU KARANTA: Mummunan hatsarin mota ya rutsa da dan majalisa daga jihar Filato

Legit.ng ta samu cewa sanarwar ta cigaba da bayyana cewa ta kwace muggan makamai daga hannun 'yan bindigar tare kuma da ababen hawan su da suka hada da kekuna kwara biyar.

A wani labarin kuma, rundunar dakarun sojin Najeriya dake sintirin tabbatar da tsaro da samar da zaman lafiya a jahohin Arewa ta tsakiya a ranar Asabar din da ta gabata sun sanar da yin kicibis da wasu 'yan bindiga a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.

Sanarwar afkuwar hakan dai ta fito ne dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na hedikwatar rundunar dake Abuja, Texas Chuku inda yace kuma dakarun nasu sun yi dauki ba dadi da 'yan bindigar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel