Tsaka mai wuya: APC da wasu jam'iyyu 15 sun yiwa Saraki taron dangi

Tsaka mai wuya: APC da wasu jam'iyyu 15 sun yiwa Saraki taron dangi

- Tun bayan ficewar shugaban majalisar dattijai daga APC ake ta yunkurin sauke shi daga kujerarsa

- Yanzu haka hadakar wasu jam'iyyu a jihar Kwara sun kudir aniyar dakile tasirin da Sarakin yake da shi gaba daya

Tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kwara wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC Iyiola Oyedepo, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta shirya tsaf tare da hadin gwiwar jam’iyyu guda 15 domin dakile tasirin siyasar shugaban majalisar dattawa Dakta Abubakar Bukola Saraki a jihar.

Jam’iyyu 15 sun dora tukunyar tuggu don kawo karshen tasirin Bukola Saraki a Kwara

Jam’iyyu 15 sun dora tukunyar tuggu don kawo karshen tasirin Bukola Saraki a Kwara

Tsohon shugaban jam’iyyar ta PDP ya zargi Bukola Saraki da rashin iya shugabanci da kuma wakilci marar amfani ga al'ummar jihar ta Kwara. Ya kuma lissafa jam’iyyun da suka yi hadaka domin yakar Sanatan, wadanda su ka hadar da:

APC da KOWA da YPP da DPC da NNPP, sauran sun hada PDC da YDP da FJP da LP da sauran jam’iyyun da suka dauki gabarin dakushe tasirin siyasar shugaban majalisar dattawan.

Oyedepo ya bayyana hakan ne a jiya Asabar a garin Ilorin yayinda dandazon ‘yan jam’iyyar APC suke masa maraba da zuwa daga Abuja bayan dawowarsa APC.

“Zan tattara jam’iyyu 15 wadanda zamu yi amfani da su wajen dakushe siyasar Saraki".

KU KARANTA: Ko a jikinmu ficewar Bukola Saraki - Lai Mohammed

Iyiola Oyedepo ya kuma ya zargi gwamnatin jihar ta Kwara da samun rabon arzikin kasa wanda ya kai zambar kudi har Naira tiriiyan 1, tare da ciwo bashi na tsahon shekaru 16. Amma duk da irin wannan makudan kudaden al'ummar jihar suna fama da matsanancin talauci da fatara gami da rashin ababen more rayuwa.

Jam’iyyu 15 sun dora tukunyar tuggu don kawo karshen tasirin Bukola Saraki a Kwara

Jam’iyyu 15 sun dora tukunyar tuggu don kawo karshen tasirin Bukola Saraki a Kwara

Amma sai dai a nasa bangaren Babban mai taimakawa gwamnan jihar Kwara Dakta Muhyideen Akorede ya bayyana cewa gwamnan jihar Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed da kuma Sanata Saraki sun samar da ingantanciyyar gwamnati a jihar.

Ya kuma kara da cewa karkashin shugabancin Abdulfatah Ahmed jihar Kwara ta samu nasarar lashe kyaututtika a matakai daban-daban.

A karshe ya kalubalanci tsohon shugaban jam’iyyar na PDP da ya kawo shaidun da za su tabbatar da cewar gwamnatin jihar Kwara ta karbi adadin kudin da ya ke ikirari.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel