Rundunar Sojin Najeriya sun damke wani cikin sahun manyan ‘Yan Boko Haram

Rundunar Sojin Najeriya sun damke wani cikin sahun manyan ‘Yan Boko Haram

- Rundunar Sojojin operation LAFIYA DOLE sun yi ram da wani ‘Dan ta’adda

- An dade ana neman Maje Lawan wanda shi ne ‘Dan ta’adda na 96 a jeringiya

- Sojojin sun kama shi ne a Banki a Borno inda ‘Yan ta’addan su ka fitina a baya

Rundunar Sojin Najeriya na Operation LAFIYA DOLE sun samu nasarar cafke wani fitinannen ‘Dan ta'addan Boko Haram wanda yana cikin manyan ‘Yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a kasar nan.

Rundunar Sojin Najeriya sun damke wani cikin sahun manyan ‘Yan Boko Haram

An yi ram da wani gawurtaccen 'Dan Boko Haram a Borno

Birgediya Janar Texas Chukwu wanda shi ne Darektan hulda da jama’a na gidan Sojin kasar ya bayyana mana cewa Rundunar Sojojin na Najeriya sun cafke Maje Lawan wanda ake zargin yana cikin manyan ‘Yan Boko Haram.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta taso wasu manyan Ma'aikatan Gwamnati a gaba

Sojojin Kasar na OPERATION LAFIYA DOLE sun kama wannan rikakken ‘Dan ta’adda ne a Garin Banki da ke cikin Jihar Borno. Lawan shi ne mai lamba na 96 a cikin sahun gawurattun ‘Yan ta’addan Boko Haram da ake nema a Najeriya.

Wannan ‘Dan ta’adda ya sab yadda yayi shiga cikin sansanin ‘Yan gudun Hijira yayi lanbo. Yanzu haka ana cigaba da gudanar da bincike wanda bayan nan Sojojin za su dauki matakin da ya dace na maka shi a hannun Hukumomin kasar.

Darektan yada labaran watau Janar Chukwu yace a jiya Asabar ne aka yi wannan gam-da-katar inda ya nemi jama’an Gari su cigaba da Sojojin Najeriya hadin kai wajen kawo karshen ta’addanci a Yankin da sauran bangarorin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel