Sanatan Kaduna ya zargi wasu manyan Jihar da kwana a otel

Sanatan Kaduna ya zargi wasu manyan Jihar da kwana a otel

Mun samu labari cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki Kwamared Shehu Sani ya jefi wasu manyan a Gwamnatin Jihar da aikata aikin kawai inda yace su na kwana a otel.

Sanatan Kaduna ya zargi wasu manyan Jihar da kwana a otel

Sanata Shehu Sani yace yana nan daram-dam-dam a APC

Sanata Shehu Sani yayi wani jawabi kwanan nan a shafin sa na Facebook inda yayi kira ga ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC su rika karanta tsarin mulki da dokokin Jam’iyyar domin gudun sabo. Sanatan yayi hakan ne bayan an dakatar da shi daga APC.

KU KARANTA: Za a yi wa wani babban ‘Dan siyasar Kaduna wankan shigowa PDP

Shehu Sani ya nuna cewa dakatar da shi da aka yi daga APC ta sabawa ka’idar Jam’iyya. Sanatan yace babu wanda ya isa ya dakatar da shi daga Jam’iyyar. Sani yace Kaduna ta tsakiya ba wurin wasan wadanda ba su kwana a gidajen su bane.

‘Dan Majalisar yayi kalamai marasa dadi a shafin na sa yana mai watsi da dakatarwar da aka yi masa. Sanatan na APC ya kuma nuna hoton sa cikin kayan atisaye inda yace ya kamata wadannan mutane su rika motsa jiki su daina kwana a otel.

Dama kun san cewa rikicin da ke tsakanin Sanatan Kaduna Shehu Sani da kuma Gwamnan Jihar Mai girma Malam Nasir El-Rufai ya kara kunno kai inda har ta kai Jam’iyya ta jadadda cewa an dakatar da Sanatan daga APC a gundumar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel