Zan goyi Bayan duk Amintaccen 'Dan Takarar Gwamna daga Mazabar Jihar Ogun ta Yamma - Obasanjo

Zan goyi Bayan duk Amintaccen 'Dan Takarar Gwamna daga Mazabar Jihar Ogun ta Yamma - Obasanjo

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, zai goyi bayan duk wani amintaccen dan takarar kujerar gwamna da ya fito daga mazabar Jihar Ogun ta Yamma a zaben 2019.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Asabar din da ta gabata bayan halartar jana'izar tsohon sakataren gwamnatin jihar, Pa Adepoju Adeyemi, a unguwar Ayetoro dake karamar hukumar Yewa ta Arewa.

Obasanjo ya ke cewa, zai goyi bayan duk wani amintaccen dan takara da ya fito daga yankin sakamakon rashin samar da gwamna tun kafuwar jihar shekaru 42 da suka gabata.

Zan goyi Bayan duk Amintaccen 'Dan Takarar Gwamna daga Mazabar Jihar Ogun ta Yamma - Obasanjo

Zan goyi Bayan duk Amintaccen 'Dan Takarar Gwamna daga Mazabar Jihar Ogun ta Yamma - Obasanjo

Cikin munakisar ta sa da jayayya ta neman gaskiya da adalci, Obasanjo yake cewa ya kamata yankin jihar Ogun ta Yamma ya fitar da gwamnan jihar na gaba.

KARANTA KUMA: Ficewa daga jam'iyyar da kuka samu nasarar zaɓe babban laifi ne a shari'a - Falana ga masu sauyin sheƙa

Tsohon shugaban kasar ya kuma yabawa gwamnan jihar mai ci, Sanata Ibikunle Amosun, sakamakon tarayyar akida da ra'ayin su ya kasance daya akan gwamnan jihar na gaba.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar sojin sama ta Najeriya ta sake samun nasar kan 'yan ta'adda na Boko Haram a jihar Borno.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel