Fadar shugaban kasa ta tabbatar da karbar tsohon gwamna a PDP kuma Sanata mai ci zuwa APC

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da karbar tsohon gwamna a PDP kuma Sanata mai ci zuwa APC

Babban mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin da suka shafi majalisar dattijai, Ita Enang, ya tabbatar da dawowar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, zuwa jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP.

Enang ya sanar da hakan ne a jiya, Asabar, a shafinsa na Tuwita tare da bayyana cewar za a yi bikin karbarsa ranar 8 ga watan Agusta a jiharsa ta Akwa Ibom.

Ina mai tabbatar da tabbatarwa da jam’iyyar APC cewar, kamar yadda muka bayyana a baya, za a karbi Godswill Akpabio zuwa APC a ranar 8 ga watan Agusta a jihar Akwa Ibom”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

An dade ana jitar-jitar cewar tsohon gwamnan zai koma jam’iyyar APC musamman ganin yadda ya cigaba da kauracewa taron jam’iyyar PDP.

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da karbar tsohon gwamna a PDP kuma Sanata mai ci zuwa APC

Enang, Akpabio da Buhari a fadar gwamnatin tarayya

A daren ranar juma’a ne wani jigo a PDP ya shaidawa jaridar The Nation cewar jam’iyyar ta aike da wakilci domin rokon shi a kan kada ya fita “amma ba zamu iya batawa gwamnan jihar, Udom Emmanuel, domin mu faranta masa ba saboda gwamna shine jagoran jam’iyya a jiha.

DUBA WANNAN: Buhari ya fake da tafiya hutu ne bayan gama kitsa yadda za a tsige Bukola – PDP

Akpabio ya yanke shawarar fita daga PDP tun ranar 24 ga watan Yuli amma sai shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya ki sanar da majalisa saboda wasu dalilan siyasa.

Tun bayan wannan lokacin ya fara nuna alamun ya bar PDP ta hanyar kin halartar taron jam’iyyar har wanda aka shirya domin karbar wadanda suka fita daga APC da suka hada har da Saraki da Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto, da gwamna Samuel Ortom na Benuwe, da sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel