Ficewa daga jam'iyyar da kuka samu nasarar zaɓe babban laifi ne a shari'a - Falana ga masu sauyin sheƙa

Ficewa daga jam'iyyar da kuka samu nasarar zaɓe babban laifi ne a shari'a - Falana ga masu sauyin sheƙa

Mun samu rahoton cewa, kundin tsarin mulkin kasa ya haramta ficewa daga kowace jam'iyya da ta ba da nasarar zabe ga 'yan siyasa matukar ba za su yi murabus daga kujerun su ba.

Shahararren lauyan nan mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana, yayin bayyana hujjar sa dangane da sauyin sheƙar wasu 'yan majaliisar tarayya daga jam'iyyar APC zuwa PDP ya ce aikata hakan babban laifi ne da ya sabawa shari'a.

Falana ya bayyana hakan ne yayin ganawa da kafar watsa labarai ta Channels TV a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ya ce sauyin sheƙar 'yan majalisar ya ci karo da tanadi na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 da kuma hukunce-hukunce na kotu dangane da lamarin.

Ficewa daga jam'iyyar da kuka samu nasarar zaɓe babban laifi ne a shari'a - Falana ga masu sauyin sheƙa

Ficewa daga jam'iyyar da kuka samu nasarar zaɓe babban laifi ne a shari'a - Falana ga masu sauyin sheƙa

Falana yake cewa, sashe na 68 cikin kundin tsarin mulki ya harmatawa duk wani dan majalisar tarayya sauya sheƙar sa ta jam'iyyar da ya samu nasarar zabe muddin bai zai yi murabus ba daga kujerar sa.

KARANTA KUMA: Sauran ƙiris a kammala babbar hanyar Kauran Namoda zuwa Birnin Magaji a jihar Zamfara

Legit.ng ta fahimci cewa, kundin tsarin mulki na 1999 ya ba dama tare da tanadi ga kowane dan majalisar tarayya ya yi murabus daga kujerar sa kafin ya sauya sheƙa zuwa wata sabuwar jam'iyyar sabanin wadda ya samu nasarar zaben a cikin ta. '

Fitaccen lauyan ya kara da cewa, kundin tsarin mulkin ya kuma haramta rabuwar kai cikin kowace jam'iyyar kamar yadda aka samu rabuwar kai cikin jam'iyyar PDP, inda Ali Modu Sheriff da Makarfi suka dara ta gida biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel