Tambuwal ya gargadi Buhari kan rikicin Majalisa bayan ya koma Jam’iyyar PDP

Tambuwal ya gargadi Buhari kan rikicin Majalisa bayan ya koma Jam’iyyar PDP

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ja kunnen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da shirin tsige Shugaban Majalisar Bukola Saraki. ‘Dan autan na PDP yace ba za su zura idanu a taba Bukola Saraki ba.

Tambuwal ya gargadi Buhari kan rikicin Majalisa bayan ya koma Jam’iyyar PDP

Gwamna Tambuwal yace APC na neman tunbuke Saraki

Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Kasar nan Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa a shirya su ke da su yaki Jam’iyyar APC mai mulki idan tayi kokarin sauke Bukola Saraki daga matsayin sa na Shugaban Majalisa.

Gwamna Tambuwal ya bayyana cewa wasu na kokarin yi wa Majalisar Kasar kutse su kuma sace sandar girma domin a daura wani sabon Shugaban Majalisar Dattawa. Tambuwal yace da alamu masu wannan shiri ba su san dokar kasa ba.

KU KARANTA: Wani babban ‘Dan PDP a ya koma APC bayan an mika PDP hannun Saraki

Aminu Tambuwal yace idan Sanatocin sun yi amanna da Bukola Saraki da Yakubu Dogara a matsayin shugabannin Majalisa babu wanda ya isa ya taba su. Tambuwal yace babu wanda ya isa ya tunbuke manyan Majalisar ana zaune kalau.

Gwamnan na Sokoto yayi wannan jawabi ne a makon jiya wajen taron da Jam’iyyar adawa ta PDP ta shirya. Tambuwal wanda ya koma Jam’iyyar PDP kwanan nan yace ba za su ji tsoron kulle-kullen da Gwamnatin APC ke kitsawa ba.

Kwanan nan PDP ta shirya taron NEC inda irin su Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da sauran wadanda su bar APC a kwanan nan su ka halarta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel