Ba zan taba goyon bayan Atiku a matsayin shugaban 'Kasa ba - Obasanjo

Ba zan taba goyon bayan Atiku a matsayin shugaban 'Kasa ba - Obasanjo

A ranar Juma'ar da ta gabata ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa kada Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa ya sa ran da goyon bayan sa a yayin da yake fafutikar sa ta neman kujerar shugaban kasa.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na Premium Times jim kadan bayan dawowar sa daga Birnin Kigali na kasar Rwanda da tsakar ranar Juma'ar da ta gabata.

Shugaban kasar yake cewa, ta ya ya zai goyi bayan Atiku bayan kar-ta-san-kar tsakanin sa da shi, inda yake cewa ba zai taba samun goyon bayan sa ba akan wannan fafutika ta neman kujerar shugaban kasa da ya shafe wani adadi na shekarun rayuwar sa ya na neman ta.

A yayin tuntubar sa dangane da goyon bayan kudirin Atiku na neman kujerar shugaban kasa, Obasanjo ya bayyana cewa Allah ma zai garface shi ba muddin ya aikata hakan, inda yake cewa "da dai ba ya da masaniya a kansa to da kuwa hakan ta tabbata."

Ba zan taba goyon bayan Atiku a matsayin shugaban 'Kasa ba - Obasanjo

Ba zan taba goyon bayan Atiku a matsayin shugaban 'Kasa ba - Obasanjo

"Sai dai a halin yanzu Atiku ba zai taba samun goyon baya na ba saboda ni na san shi ya sanni, inda yace hakan ba ya nufin kiyayya ga Atiku da wata manufa ta sa ta karan kansa."

Wannan furucin na tsohon shugaban kasar ya zo ne bayan makonni biyu da Atiku ya bayyana kudirin sa na neman kujerar shugaban kasa.

Obasanjo ya kuma yi Allah wadai dangane da mulkin kama karya na shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman yadda ke gudanar da al'amurran da suka shafi tsaro a kasar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, tsaffin shugabannin biyu sun gana a wani taro da ya gudana watan da ya gabata cikin garin Abuja, inda suka yi hannu da juna da hakan ya sanya aka fara jita-jitar Obansajo na goyon bayan Atiku.

KARANTA KUMA: Dankwambo ya karrama Tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Marigayi Hashidu

Domin jaddada matsayar sa akan rashin goyon bayan Atiku, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa muddin kana gudanar da al'amurra domin ci gaban kasar nan to ko shakka babu sai na goyi bayan ka.

Bugu da kari Obasanjo ya bayyana cewa, ko kadan ba ya tarayya ko goyon bayan wanda ba ya gudanar da al'amurran sa domin amfani da ci gaban kasar nan ta Najeriya.

Legit.ng ta fahimci cewa, kawowa yanzu tsohon shugaban kasar bai bayyana karara wanda zai marawa baya ba yayin da babban zabe na kasa ke ci gaba da karatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel