Hukumar EFCC ta sako wasu ma'aikatan hukumar JAMB a gaba

Hukumar EFCC ta sako wasu ma'aikatan hukumar JAMB a gaba

Ma'aikatan hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun sako wasu manyan ma'aikatan hukumar JAMB wadanda ake zargi da yin sama da naira biliyan 8, kamar yanda majiyar mu ta samo

Hukumar EFCC ta sako wasu ma'aikatan hukumar JAMB a gaba

Hukumar EFCC ta sako wasu ma'aikatan hukumar JAMB a gaba

Ma'aikatan hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun sako wasu manyan ma'aikatan hukumar JAMB wadanda ake zargi da yin sama da naira biliyan 8, kamar yanda majiyar mu ta samo.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fada mana cewa hukumar ta kasa fito da naira biliyan 8 na kudin shiga na gwamnatin tarayya tsakanin 2010 da 2015.

DUBA WANNAN: Dalilan da yasa dole matasan mu su shiga harkar siyasa - Fadar Shugaban Kasa

An gano hakan ne sakamakon kudi naira biliyan 7.8 da hukumar karkashin Ishaq Oloyede ta tura na kudin shiga, a nan ne gwamnatin ta tabbatar da zargin cewa hukumar ta murkushe makuden kudaden.

Majiyar mu tace rahoton bayanin kudin an binciko shi ne a watanni da suka gabata, sannan ministan kudi ta turawa hukumar EFCC domin bincike.

A yanzu dai an samar da kwamitin bincike akan rahoton kudin.

Wata majiya daga EFCC tace: "Muna duban wasu asusun banki masu shige da ficen kudi wanda muke zargi. Daga bayanin asusun, mun gano wasu jami'an da zasu taimaka mana da binciken saboda mun gano kudaden a asusun su. Nan ba da dadewa ba zamu gayyace su don amsa mana tambayoyi. Daga cikin jami'an da zamu gayyata sun hada da daraktan JAMB mai ci a yanzu da kuma daraktan hukumar mai ritaya."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel