Buhari zai samu ruwan kuri'u a jahohi 20 a zaben 2019 da bai same su ba a 2015 - Hon. Abdulmumini Jibrin

Buhari zai samu ruwan kuri'u a jahohi 20 a zaben 2019 da bai same su ba a 2015 - Hon. Abdulmumini Jibrin

Dan majalisar nan dake wakiltar mazabar Kiru da Bebeji a majalisar wakilan Najeriya Honarabul Abdulmumini Jibrin ya yi ikirarin cewa ba bu wani mahalukin da zai iya kada Shugaba Buhari a zaben 2019 mai zuwa.

Honarabul Jibrin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da manema labarai a garin Abuja, babban birnin tarayyar inda yace idan akayi la'akari dukkanin masu hankoron kalubalantar Shugaba Buhari din babu wanda ya kai shi dumbin masoya.

Buhari zai samu ruwan kuri'u a jahohi 20 a zaben 2019 da bai same su ba a 2015 - Hon. Abdulmumini Jibrin

Buhari zai samu ruwan kuri'u a jahohi 20 a zaben 2019 da bai same su ba a 2015 - Hon. Abdulmumini Jibrin

KU KARANTA: EFCC ta gayyaci babban Akawun jihar

Legit.ng ta samu cewa haka zalika ya kuma kara da cewa shugaba Buhari zai samu ruwan kuri'u daga jahohi akalla 20 wadanda ma bai samu irin su ba a zaben 2015.

A wani labarin kuma, Yayin da lamurran siyasa a kasar Najeriya ke cigaba da zafafa musamman ma bayan sauya shekar tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata dake wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso daga APC zuwa PDP abubuwa ke ta wakana.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne ma kuma muka samu labarin cewa wasu mabiya darikar Kwankwasiyyar a jihar Jigawa suka cire jajayen hulunun su tare da yin mubayi'a ga jam'iyyar ta APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel