Dalilan da suka sanya Akpabio shirin komawa APC

Dalilan da suka sanya Akpabio shirin komawa APC

Wata majiya mai karfi daga jam'iyyar PDP ta tabbatar da shirye shiryen da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, yake na barin jam'iyyar

Dalilan da suka sanya Akpabio shirin komawa APC

Dalilan da suka sanya Akpabio shirin komawa APC

Wata majiya mai karfi daga jam'iyyar PDP ta tabbatar da shirye shiryen da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, yake na barin jam'iyyar.

Idan ba'a manta ba jiya ne majiyar mu Legit.ng ta kawo muku rahoton cewar Sanatan sunyi wata ganawa ta kusan awa biyu shi da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a babban birnin tarayya, inda alamu suka nuna cewar Sanatan yana shirye - shiryen barin jam'iyyar ta PDP ya dawo jam'iyya mai mulki ta APC.

DUBA WANNAN: Za'a daina amfani da Leda a wata kasa

Wata majiyar kuma tace Sanatan yana shirin barin jam'iyyar ne saboda barazanar da gwamnatin tarayya take yi mishi na aiko masa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa idan har bai dawo jam'iyyar APC ba.

A cewar wani dan jam'iyyar ta PDP, "Abinda yake faruwa shine, jam'iyyar APC tana yi mishi barazanar aiko masa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa, idan har bai dawo cikinta ba, shi kuma baya son hakan ta faru.

"Sannan kuma muma mun roke shi akan kada ya bar jam'iyyar, amma alamu sun nuna ya tsorata da barazanar da jam'iyyar APC ke yi masa. Ya ce baya son shiga hannun hukumar EFCC ko kadan. A zancen gaskiya yana cikin tashin hankali wanda jam'iyyar APC ta kunno masa, amma muna fatan zai ji maganar mu."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel