Za'a daina amfani da Leda a wata kasa

Za'a daina amfani da Leda a wata kasa

Kasar Chile ita ce kasa ta farko a yankin kudancin Amurka da ta zata fara haramta amfani da leda

Za'a daina amfani da Leda a wata kasa

Za'a daina amfani da Leda a wata kasa

Shugaban kasar ta Chile Sebastian Pinera ya sanar da cewar sabuwar dokar zata tabbatar da niyyar kasar ta daina amfani da Ledar wacce take janyo matsaloli masu dinbin yawa ga tattalin arzikin kasa.

DUBA WANNAN: An kashe daruruwan mutane jiya a Taraba

Dokar da 'yan majalisar kasar suka rattaba hannu aka, ta baiwa kananan 'yan kasuwa tsawon shekara daya domin kawo karshen amfani da ledar ga abokanan cinikayyar su.

Yayinda su kuma manyan 'yan kasuwa dokar ta basu wa'adin watanni 6 domin kawo karshen amfani da ledar, gwamnatin kasar ta amince da su baiwa abokan cinikin su ledoji guda biyu kacal komai yawan kayan da suka saya.

A wani bangaren kuma masana kimiyya da fasaha sunce amfani da leda na da matukar illa ga lafiyar dan adam da kuma dabbobi musamman ma wadanda take kashewa da zarar sun hadiyi ledar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel