Sultan ya karyata rahoton cewa ya goyi bayan sauya shekar Tambuwal

Sultan ya karyata rahoton cewa ya goyi bayan sauya shekar Tambuwal

Majalisar sultan na Sokoto ta nisanta kanta daga wani rubutu dake yawo a shafukan zumunta wadda ke cewa Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya nuna goyon bayansa ga sauya shekar Gwamna Aminu Tambuwal daga APC zuwa PDP.

Majalisar Sultan din tayi watsi da rahoton a wata sanarwa a Sokoto, inda ta bayyana rahoton a matsayin karya.

Ta kara da cewa: “Sultan uba ne ga dukkanin Musulmai sannan kuma bashi da son zuciya.”

Sultan ya karyata rahoton cewa ya goyi bayan sauya shekar Tambuwal

Sultan ya karyata rahoton cewa ya goyi bayan sauya shekar Tambuwal

Majalisar ta kara da cewa wasu mutane da ba’a sani bane suka hada wannan raboto, ko kadan bai da alaka da ita.

KU KARANTA KUMA: 2019: Sauya sheka ba zai hana Buhari cin zabe ba – Tony Momoh

Majalisar ta kuma bukaci jama’a da su yi watsi da rahoto, inda tayiwa kasar addu’a da fatan samun zaman lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel