Fashewar Bam ta salwantar da rayukan Mutane 15, fiye da 50 sun jikkata a wani Masallacin 'Kasar Afghanistan

Fashewar Bam ta salwantar da rayukan Mutane 15, fiye da 50 sun jikkata a wani Masallacin 'Kasar Afghanistan

A yau Juma'a kimanin rayukan mutane 15 ne suka salwanta yayin da fiye da 50 suka jikkata sakamakon aukuwar mummunan hari na bama-bamai cikin wani masallaci a garin Gardez dake Gabashin Kasar Afghanistan.

Kamar yadda wani jami'in dan sanda da ya bukaci a sakaya sunan sa ya shaidawa manema labarai na jaridar Xinhua, wannan ibtila'i ya auku ne da misalin karfe 1.30 yayin da al'ummar Musulmi ke gudanar da sallolin su na Juma'a cikin masallacin Imami-i-Zaman dake birnin Paktia.

Fashewar Bam ta salwantar da rayukan Mutane 15, fiye da 50 sun jikkata wani Masallacin 'Kasar Afghanistan

Fashewar Bam ta salwantar da rayukan Mutane 15, fiye da 50 sun jikkata wani Masallacin 'Kasar Afghanistan

Yake cewa, rahotanni dangane da sakamakon binciken hukumar ya tabbatar da cewa, harin ya auku ne a sanadiyar tashin bama-bamai har kashi biyu dda ya ritsa da mutane da dama yayin da suke ibadar su cikin masallacin.

Sai dai babu tabbaci kan iyaka adadin asarar da wannan ibtila'i ya janyo sakamakon mutane da ya ritsa da su an garzaya da su asibitoci daban-daban kamar yadda jami'in dan sandan ya bayyana.

KARANTA KUMA: Sanatocin APC sun ƙara huro wuta ta tsige Saraki daga muƙamin sa

Rahotanni sun bayyana cewa, jami'an tsaro sun sanya iyaka tare da yiwa farfajiyar masallacin kawanya domin daukan matakan tsaro gami da hana manema labarai daukan rahoto

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, kawowa yanzu babu wadanda ko wata kungiya da ta yi ikirarin zartar da wannan mummunan hari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel