2019: Sauya sheka ba zai hana Buhari cin zabe ba – Tony Momoh

2019: Sauya sheka ba zai hana Buhari cin zabe ba – Tony Momoh

Tsohon ministan bayanai, Cif Tony Momoh a ranar Juma’a yace ficewar da wasu manyan yan siyasa suka yi daga jam’iyyar All Progressives Congress ba zai hana shugaban kasa Muhammadu Buhari sake nasarar zabe a 2019 ba.

Momoh wadda ya kasance jigo a APC, ya bayyana hakan a wani hiran tarho da kamfanin dillancin labaran Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito a baya cewa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Sanata Dino Melaye, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu manyan yan siyasa daga APC sun sauya sheka zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party.

2019: Sauya sheka ba zai hana Buhari cin zabe ba – Tony Momoh

2019: Sauya sheka ba zai hana Buhari cin zabe ba – Tony Momoh

Momoh yace koda ace masu sauya shekar sun iya tatarawa sabuwar jam’iyyarsu kuri’u a yankunansu, Buhari ne zai lashe zabe a yankunansu.

Tsohon ministan yace Buhari ya samu kuri’u fiye da yawancin wadanda suka sauya sheka a yankunansu da jihohinsu, cewa hakan ce zata kuma kasancewa a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Shahararren dan takara ne kadai zai iya tsige Buhari - Gwamna Dickson

Ya bayyana cewa shugaban kasar yayi kokari a matsayin shugaba kuma yan Najeriya za su nuna godiyarsu sannan su sake zabar shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel