Shahararren dan takara ne kadai zai iya tsige Buhari - Gwamna Dickson

Shahararren dan takara ne kadai zai iya tsige Buhari - Gwamna Dickson

Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, shahararren dan takara ne kadai ya kamata a ba tutar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a zaben 2019 idan har ana so a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamna Dickson ya kuma bukaci mambobin jam’iyyar da su yi aiki tare don kafa jam’iyya mai karfi da hadin kai, maimakon tsunduma a ayyukan da ka iya durkusar da makomarsu.

Shahararren dan takara ne kadai zai iya tsige Buhari - Gwamna Dickson

Shahararren dan takara ne kadai zai iya tsige Buhari - Gwamna Dickson

Dickson wadda ya yi kiran a wajen taron masu ruwa da tsaki na PDP agidan gwamnatin, Yenagoa ya kara da cewa duk wani ayyukan da ya sabama jam’iyya ka iya gurguntar da damar da PDP ke dashi a zaben 2019.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Abu Ibrahim mai wakiltan Katsina ta kudu ya ayya cewa baza’a samu zaman lafiya a majalisar dattawa ba har sai shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki yayi murabus daga masayinsa na yanzu.

KU KARANTA KUMA: Zargin mu da ake yi a fashin Offa ne ya tursasa mu barin APC - Ahmed

Ibrahim wadda ya kasance shugaban kwamitin lamuran yan sanda na majalisa, ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai a Abuja a ranar Laraba, 1 ga watan Agusta, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel