Rayuka 21 sun salwanta yayin da wani Jirgin Ruwa ya dilmiya a jihar Sakkwato

Rayuka 21 sun salwanta yayin da wani Jirgin Ruwa ya dilmiya a jihar Sakkwato

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta bayyana cewa, kimanin rayukan mutane 21 suka salwanta yayin da wani jirgin ruwa ya dilmiya cikin teku a wani yanki da shahara da aukuwar hare-haren barayin shanu a Arewacin kasar nan ta Najeriya.

Kamar yadda wani am'aikacin hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ya bayyana, Suleiman Karim ya ce Jirgin mai dauke da fasinjoji 50 ya nutse cikin tafkin ne a gundumar Gandi ta jihar Sakkwato da misalin karfe 10.00 na safiyar ranar Alhamis din da ta gabata.

A yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar AFP, Suleiman ya bayyana cewa, hukumar ta tsamo gawawwaki 17 na mata da kananan yara 4 da wannan tsautsayi ya ritsa da su.

Yake cewa, nisan kwana ya sanya sauran fasinjoji 29 suka tseratar da rayuwar su har zuwa gabar tafkin kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana.

Rayuka 21 sun salwanta yayin da wani Jirgin Ruwa ya dilmiya a jihar Sakkwato

Rayuka 21 sun salwanta yayin da wani Jirgin Ruwa ya dilmiya a jihar Sakkwato

Rahotanni sun bayyana cewa, fasinjojin na kan hanyar su ne ta komawa zamantakewar su ta kauyen Garin Kare bayan aukuwar wani mummunan hari na barayin shanu cikin watan da ya gabata da ta sanya suka kauracewa gidanjen su.

Legit.ng ta fahimci cewa, dubunnan al'ummar kauyen su tsere inda suke nemi mafaka a sansanain gudun hijira dake garin Gandi bayan aukuwar harin 'yan baranda da ta salwantar da rayukan mutane 32 tare da kone gidaje da dama.

KARANTA KUMA: Ina nan daram a jam'iyyar APC - Gwamna Al-Makura

Dilmiyewar jiragen ruwa ta zamto ruwan dare a Najeriya sakamakon rashin kula wajen gyaran jiragen ruwa da kuma daukar adadin fasinjoji da suka sabawa ka'ida musamman a lokuta na damina.

A watan da ya gabata ne, wasu 'yan kasuwa 22 suka rasa rayukan su yayin da jirgin su ya nutse cikin ruwa a gundumar Isa ta jihar Sakkwato sakamakon malalar ruwan sama mai karfin gaske.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel