Rashin Imani: Ya yi wa karamar yarinya fyade, ya harbeta da cutar kanjamau

Rashin Imani: Ya yi wa karamar yarinya fyade, ya harbeta da cutar kanjamau

Jami’an hukumar Yansandan jihar Gombe sun sanar da cafke wasu mutane su bakwai da suka kwashe tsawon lokaci suna yi ma wata karamar yarinya mai kimanin shekaru goma sha hudu fyade, inji rahoton jaridar Aminiya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin mutanen da aka kama, akwai Hamza Musa wanda a garin lalata da yarinyar ya harbeta da cutar nan mai karya garkuwan jiki, watau sida ko ace mata Kanjamau, haka zalika binciken Asibiti ya nuna yarinyar na dauke da juna biyu.

KU KARANTA: Malam Garkawy da Dalibansa zasu fito cikin koshin lafiya – Inji Sheikh Gumi

Wannan lamari ya faru ne a unguwar Poli, dake cikin karamar hukumar Yamaltu Deba, acan ne aka tafka yarinyar nan wannan aika aika, inda take zuwa yawon talla, kamar yadda mahaifinta mai suna Malam Abdullahi ya tabbatar.

Shi kuwa wannan mutumi da ake zargin harbar yarinyar da cutar Kanjamau, mai suna Hamza Musa an kama shi ne a ranar Litinin da ta gabata, a shagonsa dake kasuwar Kwadon, inda yake sayar da alawa.

Mahaifin yarinyar, Malam Abdullahi ya bayyana cewa bayan wani dan bincike da aka gudanar, sai ga shi an damko wuyar mutane bakwai, mutanen da bincike ya nuna suma sun yi lalata da wannan yarinyar a unguwar Poli.

Tuni dai Hamza ya amsa laifinsa, kuma har ma an bada belinsa, amma da zarar an kammala bincike za’a gurfanar dasu duk gaban kuliyan manta sabo, kamar yadda wani jami’in ma’aikatar walwala na jihar Gombe ya bayyana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel