Sanatocin APC sun ƙara huro wuta ta tsige Saraki daga muƙamin sa

Sanatocin APC sun ƙara huro wuta ta tsige Saraki daga muƙamin sa

Ga dukkan alamu masu karfin gaske, sanatocin jam'iyyar APC sun sake matsa lamba tare da huro wuta ta tsige Abubakar Bukola Saraki daga mukamin sa na shugaban majalisar dattawa sakamakon aukuwar sauye-sauyen sheka zuwa jam'iyyar PDP cikin wannan mako.

'Dan Majalisar na jam'iyyar APC mai wakilcin mazabar jihar Katsina ta Kudu, Sanata Abu Ibrahim, shine ya yi ambaton hakan a ranar Alhamis din da ta gabata yayin ganawa da manema labarai dangane da sauyin shekar Saraki zuwa jam'iyyar PDP cikin wannan mako.

Abu Ibrahim ya jaddada cewa, Sanatocin jam'iyyar APC su ne mafi rinjaye a majalisar dattawa saboda haka babu wata hanya da za ta ba da dama ga tsintacciyar mage ta ci gaba da jagorantar su.

A cewar sa, dole ne Saraki ya yi murabus daga kujerar sa ta shugabancin majalisar dattawa muddin zaman lafiya da kwanciyar hankali za su ci gaba da dorewa a cikin ta dangane da nasaba ta kasar nan da kuma dimokuradiyya.

Sanatocin APC sun ƙara huro wuta ta tsige Saraki daga muƙamin sa

Sanatocin APC sun ƙara huro wuta ta tsige Saraki daga muƙamin sa

Sanata Ibrahim wanda shine shugaban kwamitin harkokin jami'an 'yan sanda na majalisar, ya kuma bayyana cewa, akwai yiwuwar majalisar za ta dakatar da hutun ta kafin ranar da ta kayyade na dawowa sakamakon doka da ta bayar da dama ga 'yan majalisa 30 su warware wannan hukunci na hutu a kowane lokaci.

Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan jagorantar zaman majalisa a ranar Talatar da ta gabata inda guguwar sauyin sheka ta kada a cikin ta, Saraki ya kuma bayar da sanarwar afkawar majalisar shiga hutu har zuwa ranar 26 ga watan Satumba.

Kamar yadda shafin jaridar Leadership ya ruwaito, akwai yiwuwar Sanatocin jam'iyyar za su dakatar da wannan hutu domin tsige Saraki daga mukamin sa ko kuma tursasa shi ya yi murabus.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya shahara wajen yawon fita neman lafiya - Ben Bruce

A baya can, sanatan mai wakilcin jihar Katsina ta Kudu ya nemi Saraki akan ya fice daga jam'iyyar ta APC sakamakon ruwa da tsakin da ya yi wajen ficewar Sanatoci 14 da kuma 'yan majalisar wakilai 37 daga jam'iyyar.

Rahotanni sun bayyana cewa, a baya shugabancin jam'iyyar APC ta fara gudanar da shirye-shiryen korar Saraki daga jam'iyyar sakamakon rawar da ya taka wajen assasa guguwar sauyin sheka a ranar Talatar da ta gabata.

Sai dai Sanata Ibrahim ya yabawa Saraki dangane da ficewar sa daga jam'iyyar da cewar huta roro, kuma a halin yanzu murabus kadai ya rage ma sa wanda muddin ba haka to kuwa ba bu sauran zaman lafiya a majalisar dattawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel