Bahallatsar tsige Saraki: Sanatocin PDP sun tare a Abuja don su ba Saraki kariya

Bahallatsar tsige Saraki: Sanatocin PDP sun tare a Abuja don su ba Saraki kariya

Sakamakon yiwuwar tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki daga mukaminsa na kara ruruwa, hakan ya jefa Sanatocin sabuwar jam’iyyar da ya koma, ta PDP, cikin zullumi, inda a yanzu haka suka tare gungu gungu a babban birnin tarayya Abuja, don bashi kariya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hatta Sanatocin da suka koma jihohinsu, duk an maidosu Abuja don jiran kota kwana, musamman daga Sanatocin tsohuwar jam’iyyar da Saraki ya baro, APC, wanda ake ganin da yiwuwar zasu yi awon gaba da shi daga kujerarsa.

KU KARANTA: Matsalar tsaro a Najeriya: Karamin aikin yan siyasa ne – Inji Ministan Buhari

Sanatocin PDP zasu gudanar da wasu muhimman taron sirri a wurare daban daban don tattauna yadda zasu bullo ma lamarin, musamman duba da adadin Sanatocin jam’iyyar APC ya fi yawa fiye da na PDP.

Bahallatsar tsige Saraki: Sanatocin PDP sun tare a Abuja don sub a Saraki kariya

Bahallatsar tsige Saraki

Guda daga cikin Sanatocin PDP da ya zanta da majiyarmu ya shaida mata cewa hatta Sanatocin da suka fita kasashen waje an aika musu da gayyata, inda ake sa ran zasu shigo Najeriya a daren Asabar, don su samu halartar ganawa da shuwagabannin PDP.

Don kuwa a ranar Larabar 1 ga watan Agusta, sai da yan majalisar wakilai yan jam’iyyar PDP suka kafa suka tsare a majalisar har cikin dare don gudun kada Sanatocinjam’iyyar APC suka bude majalisar, su kuma tsige Saraki.

Zuwa yanzu dai Sanatoci da dama daga bangarorin biyu suna ta musayar kalamai da kulle kulle, inda wasu ke ganin lallai sai an tsige Sanata Saraki daga mukamin shugaban majalisa, yayin da wasu ke ganin babu wanda ya isa, shege ka fasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel