Da dumin sa: Hukumar EFCC ta gayyaci babban Akawun jihar Sokoto

Da dumin sa: Hukumar EFCC ta gayyaci babban Akawun jihar Sokoto

Kimanin kasa da kwanaki biyu zuwa uku bayan gwamnan jihar Sokoto dake a yankin Arewa ta yamma, Aminu Waziri Tambuwal tare da 'yan majalisun jihar su 18 suka sanar da ficewar su daga jam'iyyar APC zuwa PDP, har ance hukumar EFCC ta aike da sammaci ga babban akawun jihar.

Majiyar mu ta Peoples Journal ta tabbatar mana cewa Umaru Ahmad Tambuwal dake zaman Akawun jihar tuni har samun sakon na hukumar EFCC kuma har ya fara shirin zuwa.

Da dumin sa: Hukumar EFCC ta gayyaci babban Akawun jihar Sokoto

Da dumin sa: Hukumar EFCC ta gayyaci babban Akawun jihar Sokoto

KU KARANTA: Kotun kasa da kasa ta kaso jirgin karyar fadar shugaban kasa

A wani labarin kuma, A bisa dukkan alamu dai Sanata Ayo Akinyelure dake zaman shugaban hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin ganowa da kuma kai agaji a duk inda aka samu bullar tsiyayar danyen mai watau National Oil Spill Detection and Response Agency (NOSDRA) ya kammala shire-shiren sa na ficewa daga APC zuwa PDP.

Kamar dai yadda muka samu, tsohon Sanatan da kuma ke na hannun damar shugaba Buhari ya shirya fita ne saboda ya ga alamun cewa ba zai samu tikitin takara ba a jam'iyyar APC da yake so yayi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel