Kawai kayi murabus yanzu – Kungiyar matasan Yarbawa ga Saraki

Kawai kayi murabus yanzu – Kungiyar matasan Yarbawa ga Saraki

Wata kungiyar matasan Yarbawa a ranar Juma’a ta bukaci shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki da ya sauka daga matsayinsa tunda ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa People’s Democratic Party (PDP).

Da yake Magana da manema labarai a Akure, babban birnin jihar Ondo, shugaban kungiyar na kasa, Prince Dapo Adepoju yace zai zamo rashin da’a ci gaba da kasancewa Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya tunda ya sauya sheka daga jam’iyya mai mulki zuwa jam’iyyar adawa.

Shugaban matasan ya bayyana cewa da irin wannan damar ne ke ba yan siyasa damar kin bin ka’idojin zabe a ayyukansu.

Kawai kayi murabus yanzu – Kungiyar matasan Yarbawa ga Saraki

Kawai kayi murabus yanzu – Kungiyar matasan Yarbawa ga Saraki

A cewarsa, tunda APC ce ke da masu rinjaye a majalisar dattawa, PDP dake da yan tsiraru ba ita ke da hakkin shugabantar masu rin jaye ba.

KU KARANTA KUMA: Sauya shekar Saraki, Tambuwal da sauransu ya sabama kundin tsarin mulki - Falana

Ya kuma yi kira ga jam’iyyar APC da kada ta muzantawa duk dan siyasar da ya sauya sheka domin suna da ikon bin ra’ayin kansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel