"Fita APC zuwa PDP tamkar shiga kabari ne"

"Fita APC zuwa PDP tamkar shiga kabari ne"

Yayin da ake ta cigaba da ake ta cigaba da zazzafar muhawa a tsakanin 'yan siyasa a Najeriya musamman ma dangane da sauye-sauyen shaka da ake ta yi a kasar, fitaccen dan majalisar makilan nan dake zaman bulaliyar majalisa daga jihar Kano watau Honorabul Alhassan Ado-Doguwa yayi tsokacin sa.

A nasa tsokacin Honorabul Alhassan Ado-Doguwa yace dukkan wadanda suka canza shekar suka koma PDP daga APC tamkar sun kashe kan su ne sun binne da kansu.

"Fita APC zuwa PDP tamkar shiga kabari ne"

"Fita APC zuwa PDP tamkar shiga kabari ne"

KU KARANTA: Hafsoshin sojin Najeriya sun gabatar da bukatar su ga Buhari

Haka kuma a wani binciken kwa-kwaf da jaridar Daily Trust ta gudanar game da zabukan shekarar 2019 mai zuwa musamman ma ganin yadda harkokin siyasar ke cigaba da zafafa, ta gano cewa zaben shine zai zama mafi tsada a tarihin Najeriya.

Kamar dai yadda binciken ya nuna, kasafin kudin da shugaba Buhari ya aikewa majalisa na Naira biliyan 242 da za'a kashe wajen gudanar da zaben a tsakanin abunda hukumar INEC din da kuma takwarorin ta tsaro shine mafi yawa da ba'a taba kashewa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel